Galatians 3

Bangaskiya ko Kiyaye Doka

1Ya ku Galatiyawa marasa azanci! Wa ya ruɗe ku? A idanunku aka bayyana Yesu Kiristi gicciyeyye a sarari. 2Zan so in san abu guda tak daga gare ku: Kun karɓi Ruhu ta wurin kiyaye Doka ne, ko kuwa ta wurin gaskata abin da kuka ji? 3Ku ɗin nan marasa azanci ne? Bayan farawa da Ruhu, a yanzu kuma da halin mutuntaka za ku ƙarasa? 4Ashe, wahaloli dabam-dabam da kuka sha sun zama banza ke nan? Haka zai yiwu kuwa? 5Allah ya ba ku Ruhunsa yana kuma aikata ayyukan banmamaki a cikinku saboda kuna kiyaye Doka ne, ko kuwa domin kuna gaskatawa abin da kuka ji ne?

6Ku dubi Ibrahim mana: “Ya gaskata Allah, aka kuwa lissafta wannan adalci ne a gare shi.”
Far 15.6
7Ku sani fa, waɗannan waɗanda suka gaskata ʼyaʼyan Ibrahim ne. 8Nassi ya hanga cewa Allah zai kuɓutar da Alʼummai ta wurin bangaskiya, ya kuwa sanar wa Ibrahim wannan bisharar tun kafin lokaci yǎ yi cewa, “Dukan alʼummai za su sami albarka ta wurinka.”
Far 12.3; Far 18.18; Far 22.18
9Saboda haka waɗanda suke da bangaskiya sun sami albarka tare da Ibrahim, mutumin bangaskiya.

10Dukan waɗanda suka dogara ga kiyaye Doka laʼanannu ne, gama a rubuce yake cewa: “Laʼananne ne duk wanda bai ci gaba da yi dukan abubuwan da aka rubuta a Littafin Doka ba.”
M Sh 27.26
11A fili yake ba wanda zai kuɓuta a gaban Allah ta wurin Doka, domin “Mai adalci zai rayu ta wurin bangaskiya.”
Hab 2.4
12Doka ba ta dangana ga bangaskiya ba; a maimakon haka, “Mutumin da ya aikata waɗannan abubuwa zai rayu ta wurinsu.”
L Fir 18.5
13Kiristi ya fanshe mu daga laʼanar Doka ta wurin zama laʼana saboda mu, gama a rubuce yake cewa: “Laʼananne ne duk wanda aka rataye a kan itace.”
M Sh 21.23
14Ya fanshe mu domin albarkar da aka yi wa Ibrahim yǎ zo ga Alʼummai, ta wurin Kiristi Yesu, domin ta wurin bangaskiya mu karɓi alkawarin Ruhu.

Doka da kuma Alkawari

15ʼYanʼuwa, bari in yi muku misali da rayuwarmu ta yau da kullum. Kamar dai yadda ba mai kawar ko yǎ ƙara wani abu cikin alkawarin da mutane suka kafa, haka yake a wannan batu. 16Alkawaran nan fa ga Ibrahim aka faɗi da kuma wani zuriyarsa. Nassi bai ce, “da zuriyoyi ba” wanda ya nuna kamar mutane da yawa, amma “ga zuriyarka,”
Far 12.7; Far 13.15; Far 24.7
wanda yake nufin mutum ɗaya, wanda shi ne Kiristi.
17Abin da nake nufi shi ne: Dokar da aka shigar bayan shekaru 430, ba ta kawar da alkawarin da Allah ya riga ya kafa ba, har da zai kawar da alkawarin. 18Gama da a ce gādon ya dangana a kan doka ne, to, da ba zai dangana a kan alkawari ba; amma Allah cikin alherinsa ya ba wa Ibrahim gādon ta wurin alkawari.

19To, mene ne amfanin Doka? Ƙari aka yi da ita don fitowa da laifi fili, har kafin na zuriyan nan ya zo, wanda aka yi wa alkawarin, an kuma ba da ita ta wurin malaʼiku ne, ta hannun matsakanci. 20Matsakanci fa ba domin ɗaya ba ne. Amma Allah ɗaya yake.

21To, Dokar ce tana gāba da alkawaran Allah ke nan? Sam, ko kaɗan! Gama da a ce an ba da Dokar da tana iya ba da rai, hakika, da sai a sami adalci ta wurin Doka. 22Amma Nassi ya furta cewa dukan duniya ɗan kurkukun zunubi ne, don abin da aka yi alkawari, da ake bayarwa ta wurin bangaskiya cikin Yesu Kiristi, a ba da shi ga waɗanda suka gaskata. 23Kafin bangaskiyan nan ta zo, muna a ɗaure kamar ʼyan kurkuku ta wurin Doka, a kulle sai a lokacin da bangaskiya ta bayyana. 24Ta haka aka sa Dokar ta zama jagorarmu zuwa ga Kiristi don mu sami kuɓuta ta wurin bangaskiya. 25Yanzu da bangaskiya ta zo, ba mu ƙarƙashin Doka.

ʼYaʼyan Allah

26Dukanku ʼyaʼyan Allah ne ta wurin bangaskiya cikin Kiristi Yesu, 27gama dukanku da aka yi muku baftisma cikin Kiristi kuna sanye da Kiristi ke nan. 28Babu bambanci tsakanin Bayahude da Bahelene, bawa da ʼyantacce, namiji da ta mace, gama dukanku ɗaya ne cikin Kiristi Yesu. 29In kuwa ku na Kiristi ne, to, ku zuriyar Ibrahim ne, magāda kuma bisa ga alkawarin nan.

Copyright information for HauSRK